Labarai

Ingantattun hanyoyin kaucewa biyan sabon cajin kudin Banki da CBN ta kakaba

Al’amarin sanya carjin sanyawa da cire kudin da suka kai kimanin N500,000 da babban bankin CBN ya fito dashi ta janyo cece-kuce a cikin al’umma.

Duba da cewa babban bankin ya ayyana haka ne a matsayin wani bangaren na aikwatar da shirin “Cashless Policy”, rage amfani da takardun kudi.

DABO FM ta tattaro wasu hanyoyin da mutane zasu bi domin kauracewa biyan sabon Carjin da babban bankin ya kakaba.

Na Farko; Ya kamata mutane su sani, bankin CBN, ya saka cajin ne domin tilastawa mutane rage amfani kudaden takarda.

Hanyoyin sune;

Kada ku cire N500,000 daga asusunku na banki don yi wata bukata, ku karbi lambar akawunt na wanda zaku bawa kudin domin tura masu kudin kai tsaye.

Haka zalika, Kada ku yarda a baku tsabar kudi na N500,000, ku bada lambar akawunt domin a saka muku kudinku a ciki.

Ga masu shaguwa ko wani fannin kasuwanci, a shawarce, ku garzaya bankin da kuke ajiya da sunan kasuwancinku, ku nemi a baku Na’urar POS, domin karbar kudaden abokan ciniki ta hanyar karta katinsu a jikin Na’urar taku.

A kula sosai: Kada ku bawa kowa bayananku na Banki, musamman lambobin katin ATM da Lambar BVN.

A wannan marrar ta matsin lamba da ake fama da ita, za’a tatukeku a barku ba sidi ba sadada.

Comment here