Buhari bai bawa dan Fim din Hausa, Nura Hussaini mukami ba

A makon da muke ciki ne dai wasu daga cikin Kafafen Labarai na Hausa suka wallafa labarin cewa; “Shugaba Buhari ya baiwa Nura Hussaini mukami a kwamitin aikin Hajji.”

Sai dai bayan bincike da DABO FM ta gudanar, ta tabbatar cewa babu tushe ko asali a cikin labarin, hasalima sunan Nura Hassan Yakasai takardar daukar aikin ta kunsa.

DABO FM ta tabbatar da cewa Nura Hassan Yakasai da shugaba Buhari ya baiwa mukamin kwamishinan a hukumar aikin hajji, babban ma’aikaci ne a bankin UBA dake jihar Kano.

Shi ma jarumin da yake tattaunawa da Dimokradiyya TV, ya shaida cewa; “Ba’a bashi mukamin komai ba.”

“Nayi matukar mamaki a lokacin da naji wannan labarin, hankalin ya kasa dauka, kuma ban yadda da cewa nine ba ma.”

“Sunanmu ne yazo iri daya da wanda aka bawa mukamin.”

Masu Alaƙa  Kotu ta bayar da belin Sunusi Oscar 442

Jarumin yace duk da kasancewa bashi aka baiwa mukamin amma yaji dadi kuma yayi murna bisa irin addu’o’i da ya samu daga al’umma ta fatan alheri. Inda ya kara da cewa dama bai saka a ka ba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.