//
Tuesday, April 7

Kiwon Lafiya: Mutane masu kiba sunfi amfanuwa wajen warkewa daga ciwon..

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Sakamakon wani nazari mai dumi-dumi da aka gabatar a kasar Canada ya nuna mana cewa, a cikin mutane wadanda suke kwanciya a asibiti sakamakon kamuwa da ciwon nimoniya, masu kiba sun fi samun damar ci gaba da rayuwa a duniya, in an kwatanta su da wadanda suke da matsakaiciyar kiba, lamarin da ya kara shaida mana cewa, mai yiwuwa ne matsalar kiba za ta iya amfani ga mutane a wasu fannoni.

Hakan dai na nuna cewa, akwai irin ra’ayi mai ban sha’awa dangane da matsalar kiba, wato ba lallai ne matsalar kiba ta rage wa masu fama da ita tsayin rayuwa a duniya ba, wato dai a wasu lokuta mai yiwuwa ne matsalar ta kawo wa masu fama da ita dan alheri.

An gano irin wannan hali ne a yayin da ake nazarin wasu cututtukan da mutane suka dauki tsawon lokaci suna fama da su, kamar wani nau’in ciwon zuciya da na ko da masu tsanani, wato zuciya ko koda ba sa yin aikinsu sannu a hankali, amma duk da haka ba a iya cewa, kara samun kiba, wata kyakkyawar hanya ce da ke da amfani ga wadanda ke dauke da wadannan cututtuka da muka zayyana.

Masu Alaƙa  Kiwon Lafiya: Riga Kafi ko shan magani? Zabi daya don kula da lafiyar Jiki

Manazartan da suka fito daga jami’ar Alberta ta kasar Canada sun gabatar da wani rahoto da da ke nuna cewa, sun yi nazari a tsanake kan bayanan yadda aka lura da jinya ga mutane 907 masu fama da ciwon nimoniya a cikin asibitoci guda 6 da ke birnin Edmonton na lardin Alberta, a karshe dai sun gano cewa, yawan masu madaidaiciyar kiba da suka rasu sakamakon ciwon nimoniya ya kai misalin kashi 10 cikin dari, sa’an nan kuma, yawan masu kiba da suka mutu sakamakon ciwon namoniya ya kai misalin kashi 4 cikin dari.

Manazartan sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarin da aka yi a baya ya shaida cewa, ba lallai ba ne matsalar kiba ta rage wa mutanen da suke dauke da ita lokaci da suke dauka suna rayuwa a duniya. Nazarin da suka yi a wannan karo ya tabbatar da cewa, watakila matsalar kiba za ta kawo wa masu fama da cututtuka masu yaduwa dan alheri wajen fama da cututtukan.

Masu Alaƙa  Zazzabin 'Lassa' yayi sanadiyyar mutuwar manyan Likitoci 2 a Kano

Duk da haka ina dalilin da ya sa hakan? Manazartan sun yi zaton cewa, mai yiwuwa ne dalilin da ya sa masu kiba da suke fama da cututtuka suka fi samun damar ci gaba da kasancewa a duniya shi ne jikinsu na yin ajiyar abubuwa masu gina jiki da sassansa ke amfani da shi.

Amma ana bukatar ci gaba da nazari kan yadda masu kibar da ke warkewa daga cututtuka.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020