Buhari ya bada kyautar $500,000, Babura da Motoci ga kasar Guinea Bissau

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada kyautar dala dubu dari biyar, kwatankwacin Naira miliyan 180 ga kasar Guinea domin gudanar da zabubbuka dake karatowa a kasar.

Mai magana da yawun shugaban, Mallam Garba Shehu yace kasar Guinea ce ta bukaci shugaba Buhari ya tallafa mata.

“Bisa sakon tsananin bukata da kasar Guinea Bissau aikewa Najeriya na neman taimako, Shugaba Buhari ya baiwa kasar kayyakin zabe 350, Babura 10, Motar Hilux 6, Gingimari 2 da tsabar kudi $500,000.”

Ya kara bayyana cewa shugaba Buhari ya umarci Ministan Harkokin kasashen wajen Najeriya, Mr Geoffrey Onyeama, daya wakilce shi a kasar ta Guinea tare da kai ziyarar aiki kasar Kwatano.

Ministan dai zai wakilci shugaba Buhari a taron kungiyar shugabannin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS.

Ziyarar da Ministan ta bio bayane ne bayan da rikice-rikicen siyasa ya barke a kasar a lokacin da zaben ‘yan majalissu da za’a gudanar a kasar rana 28 ga watan Afirilun 2018.

%d bloggers like this: