Ganduje zai kaddamar da Manyan Motocin Bas na zamani guda 100

Gwamnatin jihar Kano, karkashin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje tace ta kammala shirinta ta kaddamar da shirin inganta harkokin zirga zirga a cikin birnin Kano.

Gwamnatin ta kaddamar da shirin kawo manyan motocin Bas Bas, wadanda zasu taimaka wajen zirga-zirga cikin birni da kewayen jihar Kano.

Motocin kirar BRT zasu kasance irin su na farko da wata gwamnati a jihar Kano zatayi wajen saukaka harkar sufuri a jihar.

Tini dai gwamnatin jihar Kano ta cimma matsaya tare da Kamfanunuwan Motocin Zhengzhou Yuong da Zhengzhou Public Bus Communication domin kawo manyan motocin guda 100 zuwa jihar Kano.

Motocin zasu kasance na zamani da kayan kayatarwa a cikinta, tare da na’urorin tsaro saboda tsare wadanda zasu hau motocin.

Gidan Talabijin na NTA ya rawaito cewa Gwamna Ganduje yace za’ayi shirin ne domin kawo sauyin tare da bawa yan kasuwa damar yin kasuwancin su cikin sauki a jihar Kano.

“A yanzu haka, jihar Kano ce tafi yawan mutane a Najeriya. Tana da mutane miliyan 16. Ana amfani da kananan motoci da barura masu kafa uku wadanda basa cikin cigaba na babban gari. Don haka dole ne a kawo cigaba na zamani. Haka zai sa Kano ta kara zama babban gari mai cigaba.

Gwamnan ya samu wakilcin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Harkar Sufuri na jihar Kano, Engr Aminu Aliyu Wudil.

Kwamishan yayi karin haske, inda yace shirin gwamnatin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi a jihar Kano, kara birantar da jihar Kano tare da rage gurbatar Iska a jihar.

%d bloggers like this: