Buhari ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki 10 a kasar Birtaniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya a yau Lahadi, 05/05/2019 daga Birtaniya bayan shafe kwanaki 10.

Sai dai har zuwa dawowar shugaban, fadar gwamnatin ta kasa bata bayyanawa al’umma dalilan yin tafiyar ba.

Hakan yasa wasu suka fara tunanin ko Buharin yaje kasar ne domin sake duba lafiyarshi.

Shugaban ya shafe kwanaki sama da 200 a kasar Birtaniyar tin daga faron shekarar 2015 har kawo yanzu.

Jaridar Punch tayi binciken kwanakin da shugaban kasar yayi a kasashen waje tin daga lokacin darewarshi karagar mulki.

Shugaba Buhari ya shafe kwanaki kwatankwacin shekara 1 da kwana 49 a cikin kasa da shekaru 4 na wa’adin zangon mulkinshi na farko.

%d bloggers like this: