Labarai

‘Yan sanda na farautar yan kungiyar ‘Sa Kai’ da suka harbe jami’an tsaro a Katsina

Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta farautar yan kungiyar ‘Sa Kai’ dake jihar Katsina bisa bindige wani dan sanda da Soja a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa; Kwamishinan yan sandan jihar Katsina, CP Sanusi Buba ya bayar da umarnin kawo ‘yan kungiyar ”Yan Sakai” wadanda suka harbe jami’in yan sanda da soja a garin Dandume dake jihar Katsina.

Rudunar ‘yan sandan tace, da misalin karfe 2 na ranar Asabar, ‘yan kungiyar “Yan Sa Kai” suka afkawa mazauna wata rugar fulani ta Rugar Kinda dake garin Dandume a kan babura tare da cinnawa gidaje wuta.

Harin da ‘yan kunigiyar sa kan suka kai zuwa grin ya tafi taba kananan yara maza, masu jerin shekaru 8 zuwa 14.

Sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isah ya fitar tace; gamayyar jami’an ‘yan sanda, Soji da ‘Yan Viglante ne suka samu damar tsayar da cigaba da gudanar da ta’adin ‘yan kungiyar “Sa Kai.”

Sanarwar tace sun samu nasarar tseratar da mutane 26 wadanda a yanzu haka suna charji ofis di Dandume.

Karin Labarai

Masu Alaka

Hotuna: An raƙashe a taron bikin canza sunan Buhari zuwa Sulaiman da wani Bakatsine yayi

Muhammad Isma’il Makama

Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya zata kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan Bindiga sun hallaka mutane 10 a jihar Katsina

Dabo Online

Katsina: ‘Yan bindiga sun sace surukar gwamnan jihar Katsina, Masari

Dangalan Muhammad Aliyu

Tirkashi!: Wani Bakatsine ya canza sunan sa daga Buhari zuwa Sulaiman

Muhammad Isma’il Makama

Fashewar tukunyar ‘Gas’ ta hallaka wasu ‘yan uwa su 8 har lahira a jihar Katsina

Dabo Online
UA-131299779-2