(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sarki Sunusi zai koma Sarkin kananan hukumomi 10 daga 44 na jihar Kano

dakikun karantawa

Biyo bayan amincewa da kara yawan masarautu da majalissar jihar Kano tayi, darajar sarkin Kano, Muhammad Sunusi na Biyu zata ragu matuka, daga jagorancin kana nan hukumomi 44 zuwa 10 na kwaryar birnin Kano kadai.

A takardar data fito daga majalissar jihar kan yadda ta tsara cire masaurautu 4 daga cikin babbar masarautar Kano ya nuna cewa; kowacce masarauta an ware mata yawan kananan hukumomi da zasu koma karkashin ikon wannan masarauta.

Kamar yadda aka tsare; za’a kara masarautun Bichi, Dambatta, Gaya da Karaye daga cikin gidan sarautar jihar Kano wadanda gwamnatin jiha zata dai-dai ta su da masaurautar Kano da mai martaba Muhammadu Sunusi na II yake mata sarki.

Kananan hukumomi 10 ne kacal zasu koma karkashin masarautar Kano wadanda suka hada da; Dala, Fagge, Gwale, Dawakin Kudu, Birni (Kano Municipal), Kumbotso, Minjibir, Nassarawa, Tarauni, da Ungoggo.

Masarautar Rano zata zamana tanada kananan hukumomi 10 a karkashin ikon ta, Masarautar zata samu kananan hukumomi 8, Karaye zata samu 7 inda Bichi zata samu 9, kamar yadda zaku gani a takardar.

Takardamar da faro asali ne tin lokacin da Sanatan Kano ta tsakiya, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya kai ziyara fadar Sarki Sunusi, inda masu biyyaya ga tsagin gwamnatin Dr Ganduje sukayi ta cece-kuce akan tarbar da Sarkin nayiwa Kwankwaso a fadar shi ta musamman.

Al’amarin ya kara tsamari ne a dai dai lokacin da Mai Martaba Sarki yayi magana akan zaben gwamnonin jihar Kano inda yace ‘

Muna kira ga dukkanin mutanen kano, mu guji abinda zai kawo mana zubewar mutuncin kasar mu, siyasa ba yaki bace, zabe ne sukeyi, wanda suka zaba suke so, a bashi, wanda basu zaba ba suyi hakura ya karbi hukuncin Allah

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog