Buhari ya kara wa’adin gwamnan babban bankin Najeriya ‘CBN’

Duba da karshen zangon mulkin gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele zuwa zango na biyu.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin tarayyar ta ce tini dai shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sunan Godwin Emefiele zuwa baban zauren majalissar wakilai da dattijai ta Najeriya.

Tin zamanin shugaba Goodluck Jonathan, gwamnan babban bankin yake kan karagar mulkin jagorancin babban bankin.

Kafin kasancewarshi babban bankin CBN; yayi aiki da bankunan masu zaman kansu na tsawon shekaru 26 a matsayin babban daraktan gudanarwa da babban shugaban bankin Zenith.

%d bloggers like this: