Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2019 na tiriliyan 8.92

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2019. Shugaba Buhari ya aikewa majalissar Dattajai akan kashe Naira tiriliyan 8.83.

Kudin ya kama Naira Tiriliyan 8.92 bayan karin biliyan 10 da majalissar tayi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ya rawaito sanyawa kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

Kamfanin yace; Shugaban Majalissar Dattijai, Dr. Bukoula Saraki tare da Kakakin Majalissar Wakilai, Hon Yakubu Dogara duk sun samu halartar sa hannun shugaba Buhari a fadar gwamnatin dake birnin tarayyar Abuja.

Sakataren gwamnatin tarayyar,Boss Mustapha da shugaban ma’aikata, Mallam Abba Kyari suma sun halarci wajen sanya hannun.

Akwai Ministar Kudi, Zainab Ahmad, Ministan kasafi da tsare-tsare, Sanata Udoma Udu Udoma, Ministan yada Labarai, Lai Muhammad, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na majalissa, Sanata Danjuma Goje.

Masu Alaƙa  Ƙurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a harkokin majalissar Dattijai, Sanata Ita Enang da takwaranshi na majalissar Wakilai, Umar El-Yakub duk sun halarcin taron.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.