(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Buhari zai jagoranci bude ayyukan gwamnatin jihar Gombe a yau Litinin

Karatun minti 1

Ana tsammatar zuwa shugaba Muhammadu Buhari a yau Litinin 27/05/2019 domin agorantar bude ayyukan da gwamnan jihar Ibrahim Hassan Dankwabo yayi.


Jihar ta cika da jami’an tsaron a burane da kewayen jihar a shirin dakon zuwan shugaba Buhari.

Jaridar Daily Trust ta rawaito garin ya cika da jami’an tsaro a wuraren da shugaba Buhari zai jagoranci bude ayyukan bayan zagaye da wakilinsu ya gudanar.

Daga cikin ayyukan da shugaba Buhari zai bude ya hada da; Babban Dakin Taro, Kofar shiga jihar Gombe, Filin Parking da Asibitin Mata da kananan yara da sauran Tituna.

Daga ciki akwai Ginin Makarantar Lafiya, reshen jami’an jiha ta Gombe, “GSU” da chanza fasalin makarantar Firamare ta Hassan da sauransu.

Ana saka ran saukar shugaba Buhari,karfe 12 na rana a filin tashi da saukar jiragen sama na GOmbe.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog