A ranar Juma’a, shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Landan domin halartar taron zuba hannayen jari tsakanin Burtaniya da kasashen Afirika a ranar 20 ga watan Janairu.
Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis.
Firaministan Burtaniya, Boris Johnson ne ya shirya taron, wanda a cewarsu zai kara hada kawunan shuwagabannin Afirika tare da bunkasa kasuwancin su wanda zai samar da karuwar alaka a tsakani da samar da ayyukanyi tsakanin al’umnar nahiyar Afirika da kasar Burtaniya.
Femi Adesina, ya bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya a ranar Alhamis ta sati mai zuwa.
A ranar Juma’a ne dai ake sa ran kawo karshen shari’ar gwamnan jihar Sokoto da jami’iyyar APC take kalubalantar nasarar gwamna Aminu Waziri Tambuwal.
Inda a daya bangaren kuma, ranar 20 ga watan Janairun 2020, kotu koli ta ayyana ranar a matsayin ranar da zata yanke hukuncin shari’ar gwamnan Kano da jami’iyyar PDP da dan takararta, Engr Abba Kabir Yusuf suke kalubalantar nasarar gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje.
