Kotu ta kwace kujerar dan majalissar APC ta bawa na PDP a jihar Imo

Wata babbar kotu dake da zamanta a garin Owerri, ta kwace kujerar zababben dan majalissar tarayya, Ugonna Ozurigbo, dake wakiltar Nkwerre/Nwangele/Njabu/Isu na jihar Imo.

A ranar Laraba, ya rubuta takardar ajiye matsayinshi na mataimakin kakakin majalissar jihar Imo.

Mai shari’a P.A Regime, ya bawa hukumar zabe ‘INEC’ umarnin baiwa Kingsley Echendu na jam’iyyar PDP takardar shaidar cin zaben dan majalissar tarayya na 2019.

Kotu tace Harrison Nwadike, wanda ya kai karar, shine halastaccen dan wanda ya lashe zaben cikin gida da jam’iyyar APC ta gudanar.

Nwadike ya kai karar jami’iyyar APC da hukumar INEC bisa aike da sunan Ozurigbo a matsayin wanda zai yi jami’iyyar takarar kujerar majalissar.

Masu Alaƙa  Zaben2019: Jim kadan bayan yi masa tiyata, mara lafiyar ya fito zabar shugaba Buhari a Jos

Nwadike ya bukaci kotun ta tabbatar dashi a matsayin sahihin dan takarar kujerar majalissar tarayyar a inuwar jami’iyyar APC, bisa dalilinshi na cewa kundin tsarin jam’iyyar bai yadda “Ci ba hamayya ba.”

Mai Shari’a ya tabbatar da takarar Ozurigbo haramtacciya ce, ya kuma bawa INEC umarnin baiwa dan takarar PDP, Echendu, wanda yazo na biyu a samun kuri’u,  takardar shaidar cin zabe.

Kotun ta tabbatar da ‘dan takarar PDP a matsayin zababben dan majalissar ne bisa dalilinta na cewa; Nwadike bai shiga zaben kowane mataki ba.

Ma’ana bai shiga zaben fidda gwani na APC ba tinda jami’iyya tace dan takararta yaci babu hamayya a wancen lokacin.

Masu Alaƙa  Zaben2019: Ba'a kama wani matashi 'dan PDP da bugaggen sakamakon zabe ba, labarin bogi ne - Hukumar 'Yan sanda

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: