Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Buhari zai jagoranci raba motocin zirga-zirga 820 a jihar Legas

1 min read

Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Legas a yau Laraba, 24/03/19 domin bude wasu manyan manyan ayyuka da gwamnatin jihar tayi.

Ofishin yada labaran jihar Legas ne ya fitar da sanarwar inda ya tabbatar tabbacin halartar shugaba Buhari wajen kaddamar da ayyukan.

Ayyukan su hada da:

  1. Katafariyar Tashar Ababen Hawa ta Oshodi.
  2. Manyan motoci 820 na zirga-zirga.
  3. Babban titin Airport, Ikeja.
  4. Makarantar kula da Iyaye Mata da kananan yara.

Motocin da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Ambode zata raba wadanda adadinsu ya kai 820, zasu zama motocin zirga-ziga a jihar Legas.

Motocin sun dauke na na’uorin sanyaya wajen (AC) tare da kyamarorin CCTV domin bada kulawa ta musamman da tabbatar da tsaron masu hawa motar.

Acikin motar dai akwai akwatinan talbijin don jin dadin masu hawa domin samun nutsuwa da kwanciyar hankali har zuwa kai wa ga inda mutum zai sauka.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.