//

Ciwon Shawara ya kashe azzalumin mai garkuwa da mutane a Zamfara da Katsina tare da yaranshi 11

0

Rikakken mai garkuwa da mutane, Alhaji T.K da wasu guggan shuwagabannin yin garkuwa da mutane sun mutu.

Rahotanni sun bayyana mutuwar tasu sakamakon barkewar cutar Shawara a dajin da suke zama cikin kasa da mako 1.

Jaridar Daily Nigeria ta binciko cewa Alhaji T.K dai yana da yara sama da 200 da suke aikin garkuwa da mutane a dajukan kusa da Birmin Gwari, Sabuwa, Faskari, Dan Musa, Jibiya har zuwa kasar Nijar.

Cutar zazzabin Yello Fever dai ya barke a wasu daga cikin jihohin Arewa, wanda ya hallaka mutane dayawa a garuruwan Bauchi da Kano, kamar yacce hukumar tsayar da yaduwar cututtuka NCDC ta tabbatar.

Masu Alaƙa  Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya - APC

Majiyoyin Jaridar sun tabbatar mata da cewa, Alhaji Auta, daya daga cikin shuwagabannin masu garkuwa da mutane, ya mutu tare da matarshi da ‘ya’yanshi guda 2 sakamakon ballewar cutar.

Haka zalika majiyar ta tabbatar da mutuwar Alhaji T.K mai shekaru 32 da wasu guggan miyagun shuwagabannin masu garkuwa da mutane 11 sakamakon barkewar zazzabin na Yellow Fever.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020