Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bude shagunan da ake siyar da kayyakin abinci da na magani yayin dokar hana zirga-zirga a jihar.
Sai dai sanarwar tace za a iya bude shagunan daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a yau Litinin.
Kwamishinan yace yin hakan yana cikin shiri da gwamnatin takeyi na sassauta dokar a kwana 2 na kowanne mako.
DABO FM ta tattara cewar kwamishinan yace dole ne masu zuwa shagunan da aka bude su bi umarnin bada tazara tsakaninsu domin kaucewa yaduwar cutar da tayi dalilin sanya dokar hana fita.
Haka zalika ya bayyana cewar a duk kwanaki 2 da za a sassauta dokar, wanda yake da dalilin fita ne kadai aka yarda ya bar gidanshi.
Daga karshe ya shawarci al’umma da su cigaba da bin matakan kariya kamar su wanke hannaye da ruwa mai gudana da sabulu da kauracewa taron cunkuso tare da kula da tsaftar jiki da ta muhalli.
