Da alama jami’an kula da ‘Gidan Zoo’ a Kano sun tsare kudin da aka tara da Babbar Sallah daga Goggon Biri

Da alama a wannan karon, jami’an dake tattara kudaden shiga na Gidan namun Daji a Kano sun kula da kudaden da suka tara a babbar Sallar bana.

Har yanzu babu wani rahoto ko labarin dake nuna wani abu ya samu kudaden da aka tattara na shiga gidan damun naji dake karkashin kulawar gwamnatin jihar Kano.

Idan ba’a manta ba dai, a watan Yulin 2019 a dai dai lokutan bikin karamar Sallah, rahotanni suka bayyana na “Hadiye miliyan 7 da wani Goggon Biri yayi a gidan namun dajin dake Kano.”

Lamarin daya janyo hankalin mutane a Najeriya dama wasu sassan duniya.

Tin dai a wancen lokacin, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta hannun mai magana da yawunta, DSP Haruna Abdullahi, ta bayyana kame wadansu daga cikin ma’aikata gidan namun dajin da suka bayyana Birin a matsayin wanda ya dakawa kudaden wawa.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.