Rahotan Dabo FM na yiwuwar dawowar Zakzaky Najeriya cikin kwanaki 3 ya tabbata

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da yiwuwar dawowar shugaban Kungiyar IMN, Sheikh Zakzaky, cikin gaggawa zuwa Najeriya.

A baya DABO FM ta rawaito cewa; Akwai yiwuwar Sheikh Zakzaky ya dawo Najeriya a kasa da kwanaki 3 da zai kara a kasar biyo bayan fargabar da kasar Indiya take yi na tarwatsa zaman lafiyar kasar.

Wakilan DABO FM dake chan birinin Gurugaram sun tabbatar da kiraye-kirayen zanga-zanga da mabiya Shi’a a kasar sukeyi domin neman a sakarwa Malamin mara.

A nata bangaren gwamnatin Najeriya ta bada tabbacin cewa; hukumomin kasar Indiya a shirye suke da su dawo tiso keyar Sheikh Zakzaky zuwa Najeriya bisa tsoron tada hargitsi da hadin fada da kungiyar take neman hada kasar Indiya da kasashen duniya.

Babban Sakataren ma’aikatar Labarai ta Najeriya, Grace Isu Gekpe ne ya bayyana matsayar kasar Indiya na niyyar dawo da Zakzaky a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.