Wasanni

Liverpool ta lashe kofin ‘Super Cup’ bayan ta mammake Chelsea a bugun Fenareti

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lashe kofin Super Copa bayan ta doke Chelsea a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Chelsea ce ta fara kefa kwallo a minti na 36 ta hannun dan wasanta Olivier Giroud.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, dan wasan kasar Senegal, Sadio Mané a farke kwallon a mintuna na 48.

Sadio Mané dai ya kara jefa kwallo ta biyu a ragar Chelsea a mintuna na 95.

Dan wasan Chelsea, Jorginho ya samu nasarar farkewa Chelsea kwallo ta biyu a mintuna na 101.

An tashi wasa canjaras bayan bugo mintuna 120, daga nan ne aka tsallaka zagayen bugun daga kai sai me tsaron gida.

Liverpool bata zubar da ko bugu daya ba, inda Chelsea ta zubar da bugunta na karshe wanda hakan ya bawa Liverpool damar lashe gasar da maki 5-4.

Dan wasa Sadio Manè shine dan kwallon Africa na farko daya jefa kwallo a wasan karshe na Super Cup tin bayan da Frederic Kanoute ya jefa kwallo a wasan tin a shekarar 2006.

UA-131299779-2