Daga kasar Nijar, wasu dalibai sun nuna murnar su ga nasarar Buhari

Karatun minti 1

A cigaba da nuna farinciki ga samun nasarar shugaban Muhammadu Buhari da ake tayi a cikin kasa Najeriya dama sauran sassan duniya inda ‘yan Najeriya suke zaune a wadancen kasashe, ko dai domin karatu, kasuwanci ko wani nauyin al’amari na rayuwar yau da kullin.

Daliban Najeriya da suke karatu a jami’ar Maryam Abacha dake garin Maradi a chan kasar Nijar, suma sun bayyana farincikinsu bisa lashe zaben shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Adamu Haruna Ahmad ya bayyana mana cewa daliban sun shirya taron ne domin taya shugaba Muhammdu Buhari murna.

Sai dai har yanzu a Najeriya, tsohon dan takarar shugaban kasa na babban jami’iyyar hamayya ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yaki amincewa da sakamakon zaben daya tabbatarwa shugaba Muhammadu Buhari nasarar lashe zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabarairun 2019.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog