Ganduje ya mayar da Salihu Tanko Yakasai bakin aikinsa, kwana 18 bayan dakatar da shi

Karatun minti 1
Salihu Tanko Yakasai

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da Salihu Tanko Yakasai, mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai na zamani.

Tin dai a ranar 11 ga watan Okotba gwamna Ganduje ya dakatar da Salihu Tanko Yakasai sakamakon wasu kalamai da ya yi na ganin zagawar shugaba Muhammadu Buhari a kan damuwa da halin kunci da ‘yan Najeriya suke ciki.

Lamarin da ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta musamman Twitter inda ‘yan Najeriya su ka yi wa gwamna Ganduje ca a kan dakatarwar.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog