//
Wednesday, April 1

Dalibi ya raba wa tsoffin malamanshi na Sakandire motocin kece raini da dubunnan Nairori

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaici cewa;

“Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne aka yi bikin murnar cikar kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Daura jahar Katsina (FGC Daura) shekaru 30 da kafuwa, taron daya samu halartar dururuwan tsofaffin dalibai da malamansu.

A yayin taron ne wani tsohon dalibin makarantar ya nuna bajinta, tare da fitar da tsofaffin daliban makarantar kunya, inda ya baje kolin wasu tsala tsalan motocin alfarma guda 7 domin rabarwa ga wasu tsofaffin malamansa.

Wannan dalibi ba wani bane illa Dakta Aminu Abdullahi Shagali, Kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, kuma shugaban kungiyar kakakakin majalisun dokokin jahohin Arewa gaba daya.

Masu Alaƙa  Zamu yanke wutar da muke baku idan baku biya kudi ba - Najeriya ta fada wa Nijar, Togo da Benin

Da yake mika motocin ga Malaman ta hannun wakilinsa a yayin taron, Shagali ya bayyana farin cikinsa da ganin wannan rana, sa’annan ya yaba da kokarin da Malaman suka yi a kansa lokacin da yake dalibin makarantar.

Malaman da suka samu wadannan kyaututtuka sun bayyana farin cikinsu, tare da fatan Allah Ya saka ma wannan dalibi nasu da albarka.

Baya ga motocin, Shagali ya raba ma Malaman kudin shan mai, haka zalika ya aika da sakon kudade ga iyalan tsofaffin Malaman makarantar da suka rasu, sai kuma suma malaman dake makarantar a yanzu sun samu ihisanin.

Bugu da kari kaakakin ya dauki nauyin gudanar da manya manyan ayyukan more rayuwa a cikin makarantar domin amfanin dalibai, malamai da ma sauran al’ummar makarantar, kamar su gyaran dakin karatu, famfunan ruwa, da sauransu.

Masu Alaƙa  Gwamnoni zasu fidda mutane miliyan 24 daga Talauci zuwa shekarar 2030

Legit.ng Hausa

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020