Copyrighted.com Registered & Protected

Takaddama ta barke tsakanin Shehu Sani da S Tanko Yakasai

Takaddama ta barke tsakanin tsohon sanata Shehu Sani da Salihu Tanko Yakasai a shafin twitter.

DABO FM ta binciko wani dan rikici irin na siyasa wanda ya faro asali ne da wani rubutu da Shehu Sani yayi akan chanzawa babban filin wasa dake Abuja suna zuwa Abiola Stadium da shugaba Buhari a ranar 12 ga Yuli.

Shehu Sani ya soki lamirin chanza sunan, inda yayi kira da gwamnatin Buhari da kada da rika chanza sunayen abinda wani yayi, ta bari idan ta gama sabon aikin da tayi, sai ta saka sunan wanda take so.

Bayan kalaman Shehu Sani, daga nan ne daga cikin masu kula da shafukan yada labaran fadar Shugaba Buhari a fannin, Tolu Ogunlesi, yayi masa martani.

Masu Alaƙa  Tsohon Sanata yafi wanda zuri'ar su basu taba yin Kansila ba - Martanin Shehu Sani zuwa Tanko Yakasai Dawisu

“Ba damuwa Yallabai, saboda aikin da kayiwa mutanen yankinka, ba dare ba rana, a lokacin da kake sanata, zamuyi kokarin ganin cewa an saka sunan ka da zarar an kammala titin jirgin kasa na Lagos- Ibadan.”

Shima a nashi bangaren, Shehu Sani yayi martani da “Bisa gudunmawar da kake bayarwa a sohiyal media, Kai kafin dacewa da a saka sunanka tinda a garin kune.”

Masu Alaƙa  Sanatoci sun aminta da kudirin Shehu Sani akan mayar da Kadpoly zuwa Babbar Jami'ar Fasaha

Daga nan ne, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano a fannin labarai, Salihu Tanko Yakasai ya magantu akan lamarin.

DABO FM ta binciko Yakasai yana cewa; “Tsohon Sanata bakada kirki”

Take Shehu Sani yayi kakkausar suka a fusace yace; “Tsohon Sanata yafi wanda zuru’an su kaf basu taba yin ko kansila ba.”

Salihu bai tsaya nanba, sai yayi martani da “Tayi zafi kenan.”

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: