Sanyi: Gwauraye masu kwanan Shago, yin matashi da Galan, wanka da Buta abin tausayi ne -Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, malamin addinin Islama a arewacin Najeriya, ya bayyana Maza wadanda basu da aure a matsayin abin tausayi a irin wannan lokaci na sanyi.

DABO FM ta tattaro Malamin ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da wata nasihar kai tsaye a shafinshi na Facebook, jiya Juma’a a wani filin tashi da saukar jirage da DABO FM bata iya gane sunanshi ba.

Sheikh Daurawa ya faro bayanai tare da nasihohin kokarta cika bautar Allah musamman tashi zuwa Sallar Asuba duk da tsananin sanyi da ake fuskanta.

DABO FM ta tattaro cewar a dai dai lokacin da Malamin ya kammala addu’a ya mika tausayinshi ga wadanda basu da aure, wanda basa samun masu tashinsu da asuba balle akai ga dafa musu ruwan zafi.

Masu Alaƙa  Ana ta kama masu wakokin nanaye an bar masu barna da sunan addini suna zagin Allah - Sheikh Daurawa

“Allah Ya karbi ibadunmu a wannan yanayi, Ya kuma bamu kwarin gwiwa. Su kuma tuzurai, gwauraye marasa Aure, da masu kwanan shago, muna fata Allah Ya rufa muku asiri kafin sanyi mai zuwa yana da kyau ace kowa ya shiga daga ciki.”

”Nasan abin tausayi a wannan zamani, musamman gwagware marasa aure da tuzurai da suke kwana a shago, suke kwana a zaure, suke kwana Kai da Kafa, suke tada kai da galan. Suke wanka da Buta mai lita 5.

Irin wadannan ne idan sukayi mafarki, ko kuma sun tashi da asuba zasuyi ana tsananin sanyi zai yi alwala, bashi da matar da zata dafa nasa ruwan zafi, wannan shine abin tausayi.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.