Yaushe Kwankwaso zai yi Allah wadai da kamun Abu Hanifa Dadiyata da Salisu Hotoro?

Mutane da yawa musamman masu hamayya da tsohon gwamnan Kano, Dr Rabi’u Kwankwaso, sun tofa albarkacin bakinsu kan yacce suka ce Kwankwason yaki cewa komai tin bayan neman da akayiwa wasu ‘yan gwagwarmayar tafiyar Kwankwasiyya.

Tin dai a makonnin da suka gabata ne aka kama Salisu Yahaya Hotoro, wanda ake zaton jami’an hukumar DSS suka kame shi.

A daren ranar Juma’a ne dai rahotanni suka bayyana cewa jami’an da ake zaton DSS ne sukayi awon gaba da Abu Hanifa Dadiyata.

A fagge siyasar arewacin Najeriya, za’a iya cewa Abu Hanifa Dadiyata da Salisu Yahaya Hotoro suna daga cikin manyan matasan siyasa masu kare darikar ta Kwankwasiyya.

Masu Alaƙa  Yaushe Kwankwaso zai yi Allah wadai da kamun Abu Hanifa Dadiyata da Salisu Hotoro?

Ma’abota amfani da shafin Twitter, zasu tabbatar da cewa Abu Hanifa Dadiyata, ya kasance dan gwagwarmaya mai kare muradin Kwankwasiyya da sukar gwamnatin APC a jihar Kano da ma kasa baki daya.

Inda a bangaren guda, Salisu Yahaya Hotoro yayi shura a shafin Facebook wajen kare muraden na Kwankwasiyya tare da sukar gwamnatin Gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje.

Sai dai masu adawa da tafiyar ta Kwankwasiyya sun bayyana kokensu kan cewa Engr Kwankwaso baya nuna alhini idan aka kama mabiya darikar ta Kwankwasiyya.

Har ma sukance a lokacin baya da aka kama Hotoro, gabanni zaben gwamnan Kano, baice (Kwankwaso) bai ce komai ba.

Zaku iya bayyana ra’ayinku a kasan wannan rubutun.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.