Eden Hazard ya kammala komawa Real Madrid

Kungiyar kwallo kafa ta Chelsea da Real Madrid sun cimma matsaya akan cinikin dan wasa Eden Hazard na kungiyar ta Chelsea.

Hakan na zuwa ne bayan da kungiyara Chelsea ta wallafa a shafinta na yanar gizo, inda ta bayyana dukkanin kungiyoyin sun cimma matsaya akan siyarwa da Real Madrid dan wasan.

Itama a nata bangaren, Real Madrid ta wallafa a shafinta na Instagram inda tace “Eden Hazard ya zama dan wasan Real MAdrid.”

Kungiyar Chelsea tace ta wallafa bayanan ne bisa kammala cinikin, idan har ya sanyawa Real Madrid hannu tare da yin gwajin lafiya.

Daga Shafin Real Madrid a Instagram

Masu Alaƙa  Magoya bayan Real Madrid sun yiwa Hazard ihun "Mu Mbappe muke so"

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.