EFCC ta janye tuhumar ta akan badakalar biliyan 25 ta Goje bayan ya janye daga neman shugaban majalissar dattijai

Ofishin Minitsan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayyar na kasa ya karbe ragamar takaddamar Danjuma Goje dake gaban Kotu akan tuhumar yin sama da fadi da Naira biliyan 25 daga hannun EFFC.

Ranar Alhamis dai Goje ya janye daga neman shugaban majalissar Dattawan Najeriya bayan ya gana da shugaba Buhari a fadar gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya rawaito cewa hukumar EFCC ta shafe shekaru 8 tana tuhumar tsohon gwamnan a kotu har zuwa Juma’a da zata dena.

Takaddamar shari’ar dake gaban mai shari’a Babatunde Quadiri na kotun tarayya a Jos II.

Bayan an kotu ta kira zaman gaggawa a gaban mai shari’a Quadri, lauyan EFCC, Wahab Shittu, ya bayyanawa kotu cewa zasu janye hannun daga cikin takaddamar tare da mayar da ita karkashin ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya.

“Ya mai shari’a, an dage cigaba da sauraron wannan shari’a zuwa 20 ga watan Yuli, sai dai yau gamu domin mu fadin inda aka kwana akan batun.”

“Daga bangaren EFCC, zamu janye wannan takaddama daga hannunmu zuwa ga ofishin babban lauyan tarayyar domin cigaba da hukunci.”

“Kamar yadda yake yau a Kotu, doka ce daga ofishin ministan shari’a na kasa cewa su zasu karbe ragamar dukkanin al’amura daga hannu mu.” -Inji lauyan EFCC

%d bloggers like this: