Home LabaraiEFCC sun kai sumame gidan Abdulaziz Yari na Zamfara

EFCC sun kai sumame gidan Abdulaziz Yari na Zamfara

by Dabo Online
0 comments

A ranar Lahadi, Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kai sumame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, zuwa gidanshi dake Talata Mafara.

Shaidun gani da Ido sun tabbatar da faruwar al’amarin tare da bayyana cewa jami’an sama da guda 20 sunzo a motoci 7 wanda suka hada da babbar mota kirar ‘BUS.’

Jaridar Daily Nigerian ta tabbatar da faruwar al’amarin inda ta tabbatar cewa shaidun gani da idon sun bayyana mata ‘Jami’an sun gudanar da binciken na tsawon awanni 5.

“Mun tattaro cewa; Jami’an sunzo gidan wajejen karfe 6 na yamma, sun tafi karfe 11 na dare.”

Har yanzu dai ba’a samu tabbacin cewa hukumar da samu daukar wani abu ba a lokacin da suka gudanar da aiki a gidan.

Majiyoyi sunce ba’a samu Abdulaziz Yari da Iyalanshi a cikin gidan ba.

Mutanen da ke rayuwa a wannan yankin, sun fito sunyi cirko-cirko a kusa da gidan tare da yin Tabarbari suna ”Allahu Akbar, Allahu Akbar….”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00