Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar suka yi wacce ke kalubalantar nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ya gudana.

Kungiyar alkalan bakwai na babbar kotun da ta samu jagorancin Jastis Tanko Mohammed, shugaban alkalan Najeriya, ta ce, sun sakankance cewa babu wani amfani game da daukaka karar. A don haka ne suka yi fatali da karar.

Shugaban alkalan Najeriya, Jastis Tanko, ya kara da cewa, kungiyar alkalan ta duba tare da yin nazari akan shari’ar tun kusan makonni biyu da suka gabata. Ya ce, za a sanar da dalilin watsi da karar a ranar da kotun zata sanya.

Masu Alaƙa  Buhari ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki 10 a kasar Birtaniya

Atiku da jam’iyyarsa na kalubalantar hukuncin ranar 11 ga watan Satumba ne wanda ya samu jagorancin Jastis Mohammed Garba a kotun sauraron kararrakin zabe.

Karar kuwa na kalubalantar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a zaben shugabancin kasa da ya gabata.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.