EFCC ta kama Kanin sakataren gwamnatin jihar Zamfara da miliyan 60 a wani gida

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama tsabar kudi Naira miliyan 60 a gidan dan uwan sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi.

EFCC ta kama Murtala Muhammad, a gida mai lamba 145 dake kwatas din Igala a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

EFFC ta kwace mota kirar Toyota mai launin baki da lamba DKA 67PX Kaduna, tare da manyan jakunkunan “Ghana Must Go” guda hudu masu dauke da rafar naira dubu dubu na miliyan 15 a cikin kowacce jaka, wanda ya hada miliyan 60 baki daya.

Bindigar turawa kirar “Single Barrel”, bindigar gargajiya da damin harsasai 25.

Sako na musamman

Masu Alaƙa  Mai maganin gargajiya ya damfari wani dan Koriya ta Kudu miliyan 30 akan zai nemo masa lasisin NNPC

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: