Wata babbar Kotu ta dakatar da umarnin kama akantan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Karatun minti 1

Wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da umarnin kamun da wata karamar kotu tayi na kama shugaban ma’aikatan fadar Sarkin Kano da wasu mutane 2.

An dai kai Shugaban ma’aikatan wanda yake da mukamin Danburan Kano, tare da Mujitaba Abba da akantan masarautar, Sani Muhammadu Kwaru gaban kotun daga hukumar karbar korafe da yaki da cin hanci rashawa ta jihar Kano bisa rashin amsa gayyata akan binciken da akeyiwa sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II , na salwantar da naira biliyan 4 na masarautar.

A hukuncin kotun ta ranar Talata, mai shari’a Muhammadu Idris ya bada umarnin kame mutanen 3 bisa rashin amsa gayyatar hukumar.

Sai dai a ranar Talata, wata babbar kotu ta karkashin jagorancin banban  mai shari’a ta dakatar da shirin kamun, tare da bada umarnin jin ta bakin kowa daga cikinsu.

Kotun dai ta saka ranar 13 ga watan Yuli domin sauraronsu gabaki daya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog