Kwankwaso ya tura matasa neman Ilimi, Ganduje ya bude cibiyar koyar da gyaran mota

A daidai lokacin da Gidauniyar Kwankwasiyya take rakiyar tura cikon matasan da ta dauki nauyin karatun zuwa filin jirgi domin tafiya makaranta, ita ma gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta bude sabon garejin wanke mota.

DABO FM ta tattara cewar gwamnatin Dr Andullahi Ganduje ta bude gareji domin amfanar matasan da gwamantin ta dauki nauyin koyar dasu aikin gyaran motoci a kamfanin Peugout na jihar Kaduna.

A shekarar 2018, gwamatin jihar ta tura matasa 422 domin samun horon gyaran motoci a kamfanin dake jihar Kaduna.

Haka zalika, Gidauniyar Kwankwasiyya, a yau Alhamis ta karasa tura daliban da ta na cikon 370 da ta dauki nauyin kammala karatunsu na digiri na 2 a sassa daban daban na fadin duniya.

Masu Alaƙa  Kano: Cin Hanci: Ganduje ya rabawa wasu ma'aitakan INEC filaye

Dabo FM ta tattara cewar daliban guda 7 zasu yi karatu a fannin ilimin addinin Islama da harshen Larabci a kasar Sudan yayin da sauran 2 zasu karanci fannin kasuwanci a birnin Dubai.

A watan Satumbar da Oktobar 2019, daliban gidauniyar sama da 240 suka sauka a kasar Indiya domin yin karatu a wasu daga cikin manyan jami’o’in kasar da suka hada da Sharda Univeristy.

Haka zalika DABO FM ta samu ziyartar daliban a lokacin da tsohon Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai wa daliban ziyara a birnin Greater Noida dake jihar Uttar Pradesh kusa da babban birnin New Delhi a ranar 5 ga Nuwamba a 2019

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.