Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya sanya dokar ta-baci a kananan hukumomin Kaura da Jema’a sakamakon rikici-rikici da suke faruwa a yankin.
Hakan na zuwa bayan neman da jami’an tsaro suka yi domin a fadada dokar ta-baci zuwa kananan hukumomin biyu.
DABO FM ta tattara cewa kafin fadada dokar, akwai dokar a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.
Gwamnan ya sanar da sabuwar dokar a shafinsa na Twitter a jiya Juma’a.
A makon da ya gabata dai an samu karuwar rikice-rikice a yankunan Zikpak da Unguwar Masara.