Labarai

Yanzu an mayar da sarakuna a Kano basu da wata daraja -Aminu Daurawa

Babban malamin addinin musulunci kuma tsohon kwamandan Hisba ta jihar Kano, Malam Aminu Daurawa ya bayyana cewa gwamnata tasa an dena ganin darajar sarakuna.

Rahoton mu na nan Dabo FM ya bayyana cewa Malamin ya furta haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da jaridar DailyTrust a garin Lagos.

“A baya sarakuna na da daraja da muhimmanci” inji Daurawa.

Daurawa yace “Yadda aka yi lamarin bisa gaggawa ba tare da an bai wa jama’a dama ba duk da cewa wannan zamani ne na mulkin dimokuradiyya ba lokacin mulkin kama karya ba.”

“Don haka mu a fahimtarmu rashin yin shi ya fi alheri, a bar al’umma ta zam daya shi ya fi alheri.”

“Domin yanzu babbar matsalar da ake ciki a Kano gori ya fara shiga tsakanin al’ummar da ke bangarorin Kano. Wannan yana sarkinmu ya fi, wancan yana namu ya fi.”

“Yanzu za ka ga mutanen wannan yanki suna kushe wancan sarkin, haka su ma wadancan suna kushe na wannan har sarautar ma ta zama tamkar siyasa.”

“Wannan in zai yi wani abu ya ce wancan sarkin zan gayyata, sai a gayyato wani sarki ya shigo masarautar wani.” Inji Malam Aminu Daurawa.

Masu Alaka

An so bawa hammata iska lokacin da Ganduje ke fitar da jagorancin jam’iyyar APC

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje ya bijirewa umarnin Kotu, ya nada sarakuna 4 daya ƙirƙira

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Dama nasan za’a rina, tallafin Ganduje wajen ruguza Ilimin ‘yan Sakandire, Daga Nazeef Touranki

Dabo Online

Gwamnatin jihar Kano ta dawo da dokar hana cakudar Maza da Mata a baburan ‘Adaidata Sahu’

Dabo Online

Jirgin Kasa ya bi takan wasu mutane a jihar Kano

Gwamnoni 17 daga cikin 29 ne zasuyi Bikin cika kwanaki 100 babu Mukkarabai

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2