Zabbaben dan majalissar da Kotu ta kwacewa kujera, Kawu Sumaila ya kaddamar da fara tafsirin Azumi

Zababben dan majalissar tarayya da wata kotu ta kwacewa kujera, Hon Abdurrahman Kawu Sumaila, ya kaddamar da fara tafsirin azumin Ramadan na bana.

Tsohon babban mai bawa shugaba Buhari shawara a harkokin majalissar tarayya, ya bude karatun ne jiya a garin Sumaila dake jihar Kano.

Hon Kawu Sumaila yayin gudanar da Tafsiri

A makonnin da suka gabata ne dai wata kotu ta kwace kujerar wakilcin karamar hukumar Takai/Sumaila daga hannun Kawo bisa tabbatar da rashin fafatawarshi a zaben fidda gwani da akayi a jami’iyyar su ta APC.

Kawu dai ya nemi tsayawa takarar Sanata, inda ya kara da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

%d bloggers like this: