Ganduje ya gwangwaje Zainab Aliyu da Naira Miliyan 3 bayan fitowarta daga hannu Saudiyya

Karatun minti 1

Mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar tsabar kudi har Naira Miliyan 3 ga kowanne su.

Gwamnan ya bada kudin ne a yau Laraba bayan Shugabar hukumar mai kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Hon Abike Dabiri ta dankawa gwamnan Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar wadanda suka samu kubuta daga zargin shiga da kwayoyi kasar Saudiyya.

Hon Abike Dabiri ta wakilici gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen ganin an dawo dasu jihar su ta Kano cikin koshin lafiya.

Shima a jawabin nashi, gwamnan ya yabawa gwamnatin tarayya dama duk wadanda sukayi hubbasa wajen ganin an kubutar da su.

Ya kuma bayyana basu kyautar Naira Miliyan 3 ga kowannen su kamar yadda, mataimakin gwamnan a fannin labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog