Bayan maganganu da tuhumar mantawa da talaka, a karshe, Dr Pantami ya fashe da Kuka

A cigaba da karatun tafsirin Al-kur’ani mai girma da Sheikh Dr Isa Ali Pantami yake gabatarwa a cikin watan Ramadan, wanda yake gudanarwa a garin Abuja, jiya 9 ga watan Ramadan, 1440, Pantami ya fashe da kuka yayin karatun.

Sheikh Pantami yayi kukan ne bisa Aya ta 63 cikin Suratu Maryam, wanda Sheikh ya kasa fassara ayar dalilin kukan daya keto masa tare da alaramma mai jan baki. Ana cikin kukan ne Sheikh ya gintse karatun tare da yin addu’o’in karin takawa da zaman lafiya.

Kalli bidiyon kukan

Danna alamar Play domin kallon Bidiyon.

Daga cikin dalilan kukan Sheikh shine mas’alar “Takawa” da Mallam yake magana akai, inda Mallam yace duk wanda ya shiga cikin tsanani ko damuwa; indai yayi Takawa, to lallai Allah zai bashi mafita.

Masu Alaƙa  Yunwa, Talauci, Tashin hankali da bala'i kawai ake fama dashi a Najeriya - Sheikh Muhd Nasir

Mallam yayi jan hankali ga al’umma dasu rike ‘Takawa’ domin tana kara kusanci ga Allah (Subhanahu wata’ala), tana kara arziki, Ilimi da nutsuwa a cikin wannan duniyar ta Allah.

Ya koka kan yadda zamanin Najeriya ta tabarbare, inda duk ake samun matsalal-tsalu na rashin tsaro da sace-sacen mutane da yin Luwadi.

“Ka san cewa ita Takawa bayan mutuwarka tana kula da zuriyarka?
Wallahi mai Takawa ma bayansa baya lalacewa. Kamar yadda Allah ya fada a cikin Kur’ani, Suratu Nisa’i, aya ta 9 Allah.

Daga karshe yayi kira cewa mutane suji tsoran Allah, domin Allah baya tsoron kowa.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Masu Alaƙa  Duk wanda yace komai yana tafiya dai-dai a Najeriya, 'Makaryaci ne Munafiki' - Sheikh Gumi

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: