Jami’an tsaro sun tsare wani Malami bayan ya soki Buhari da gazawar Gwamnatin akan matsalar Tsaro

Karatun minti 1

Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci Malam Aminu Usman wanda aka fi sani da “Abu Ammar” zuwa ofishin ta a jihar Katsina, inda kuma bayan zuwan Malamin, jami’an suka tsare shi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an kama Abu Ammar ne a jiya talata, sai dai wasu majiyoyin sunce kamun bashi da alaka da suka da caccaka da yayiwa shugaba Buhari bisa gazawar gwamnatinshi wajen yin abinda ya dace a kasa musamman matsalar tsaron kasar.

Wakilin Daily Trust yace; dai dai lokacin da Abu Ammar yake tare da abokinshi, Mallam Shamsu, jami’an DSS suka kira malamin a waya tare da bashi sakon gayyata zuwa ofishin su domin amsa tambayoyi.

“Ya amsa kiran nasu, yaje ofishin tare da Malam Shamsu, sai dai gaf da lokacin buda baki, jami’an DSS din suka umarci Malam Shamsu da ya tafi.

An dai tabbatar da faruwar al’amarin ne bayan da wakilin Daily Trust ya tattauna da ‘dan Malam Aminu, wato Murtala a lokacin da ya kai ziyara gidan Abu Ammar dake Filin Samjin cikin garin Katsina.

Sai dai hukumar ‘yan sandan jihar tace batada masani akan al’amarin ta hannu mai magana da yawun rundunar reshen jihar Katsina, SP Gambo Isah

Karin Labarai

Latest from Blog