Labarai

Ganduje ya janye biyawa Dalibai kudin jarrabawar NECO

Gidan Rediyon Dala FM dake birnin Kano ya rawaito cewa Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Ganduje ya janye biyawa dalibai kudin jarrabawar NECO.

“Gwamanatin jihar Kano ta bayyana cewa daliban da suka samu darusa 5 ko fiye da suka hada da Turanci da kuma lissafi ne kawai za su ci gajiyar biyan kudin jarrabawar kammala sakandare ta NECO a wannan shekara da gwamnatin za ta biya.

Kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano Hajiya Aisha Jafar ce ta bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, tana mai cewa muhimmancin da ilimi ke da shi ne ya sanya gwamnatin daukar wannan mataki na biya wa wadanda suka ci darussa 5 kudin na NECO.”

Tin kwana 2 da suka wuce aka fara jiyo kishin-kishin cewa dalibai suna zuwa makaranta domin ayi musu rijistar jarrabawar kamar yadda gwamnatin ta bada sanarwa.

Sai dai yaran sunce shuwagabannin makarantar suna korarsu tare da umarnin cewa karsu fadawa iyayensu.

Suma shuwagabannin makarantar sunyi kira ga Gwamnati data fito kafafen yada labarai ta fada kai tsaye cewa ta janye kamar yadda ta aiyana zata biya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarkin Kano, Sunusi II ya mayarwa da Ganduje martani a karon farko

Dabo Online

Kungiyoyin ‘masu kishin Kano’ guda 35 sun nemi in ya sauke Sarki Sunusi – Ganduje

Dabo Online

Kano: Cin Hanci: Ganduje ya rabawa wasu ma’aitakan INEC filaye

Dangalan Muhammad Aliyu

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

Gwamnatin jihar Kano zata fara biyan albashin N30,000 a watan Disamba

Dabo Online

Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Dabo Online
UA-131299779-2