Taskar Matasa

Wasu ‘yan Siyasar suna amfani da Jahilcinsu wajen Jahilartar da Matasa, Daga Umar Aliyu Fagge

MATASHI:- Shi ne mutumin da ya tasa ko ya fara mallakar hankalin sa a tsakanin shekarun samartaka {puberty age}, wannan shi ne lokaci mafi wahala ga iyaye gurin tabbatar da tarbiyar da suke kokarin kimsawa yayan su. Domin lokaci ne da yake tabbatar wa da iyaye da alumma cewa zasu amfana da wannan matashi ko kuma matsala ne ga daukacin alumma.

Matashi akili mai tunani arziki ne ga kowace alumma kuma da ire-iren wadannan matasa ake amfani gurin kawo ingantaccen cigaba ga daukacin alumma kamar yadda muke gani a wasu sassan.

KARATU:- Wannan wani tsari ne da masana suke amfani dashi gurin ilimantar wa domin alumma su fahimci abubuwan da basu sani ba, wanda hakan yakan samar da ingantacciyar alumma abar alfahari a duniya.

Idan har alumma ta kasance mai neman ilimi zai yi wuya ka sami wannan alummar cikin aikata lefukan 6arna da masha’a.

YAN SIYASA:- Kalmar siyasa ba bakuwar kalma bace a kunnuwan mu, tun iyaye da kakanni muke ji kuma muke gani yadda ake aiwatar da harkokin siyasar.

Kamar yadda muka gani a yan kwanakin na yan siyasa wasu gungun mutane ne masu neman alumma su sahale musu domin suja ragamar wannan alummar na zuwa wani lokaci, wasu yan siyasar na neman sahalewar alumma cikin lumana a inda wasu suke furta cewa zasu samu nasara ta kowane hali.

Wasu daga cikin siyasar wannan zamanin suna yin amfani da jahilcin su gurin jahiltar da samari ta hanyar hana su neman ilimi, makwadaitan samari na fadawa komar fajiran yan siyasar ne ta hanyar neman abin duniya {Kudi} daga hannun su.

Wadannan yan siyasa suna bawa kwadaitatun matasan kudi ne don suyi amfani dasu gurin yada manufar su ga iyayen gidan su a siyasance, sai kaga matashin da kake tunanin mai hankali ne ya 6uge da rubata shirme, bara, banbadanci da tumasanci a shafin sa na sada zumunci wai da sunan soyayya!

Har yanzu wasu mutanen da dama basu san me kafar sada zumunta take nufi ba shi yasa suke rubutu maras kai ballantan gindi, cikin sauki kana fadawa mutane cewa kai maroki ne dan tumasanci.

Ka ta6a ganin dan wanda kake rubutu akan sa, yayi rubutun cewa a bawa alumma ingantaccen ilimi ko ruwan sha?

Me yasa kullum irina irinka ne suke yin 6a6atun sai wanarabul wane, a gurin taron daurin aure ko wasu bukukuwan?

Idan sunyi amfani da kudin alumma gurin azurta kansu da yayan su, to me zai hana kayi amfani da tunanin da Allah ya baka gurin azurta kanka da ilimi ko neman na kanka?

Ka ta6a ganin haramun tayi tsawon rai?
Idan ma tayi to da sannu za tayi mummunan karshe, tunda ance karshen alewa kasa!

Dole matasa su bar aikata banbadanci da tumasanci da sunan siyasa, idan har suna so su mori rayuwar su a yau da gobe. Kuma idan har tumasanci ba aikin kaskanci ba ne to kamata yayi muga yayan kwamishinoni da yan majalisu suna yi, babu wani mahaluki da ya isa ya azurta ka ko ya talauta ka Allah ne kadai yake da wannan ikon.

Duk romon bakin da dan siyasa zai maka yaudara ce domin har yanzu shima bai kosa da abin duniya ba.

Rattabawa
Umar Aliyu Musa
Oumaraliyu@gmail.com

Karin Labarai

Masu Alaka

Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Gidauniyar wasu ‘yan mata a Kano ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Dabo Online

Zuwa ga masu neman a baiwa Mata limancin Sallah da nufin ‘Kare hakkin Mata’ daga Bin Ladan Mailittafi

Dabo Online

Ra’ayoyi: Bai wa diyarka jari, yafi kayi mata tanadin shagalin biki, Daga Idris Abdulaziz

Idris Abdulaziz Sani

‘Yar Najeriya mai shekaru 21 tayi fice bayan kammala karatun kiwon lafiya a kasar Turkiyya

Dabo Online
UA-131299779-2