Ra'ayoyi Siyasa

Ko mutanen Arewa zasu so Kwankwaso irin soyayyar da Buhari ya samu?

Kullin al’amuran siyasar Najeriya suna kara chakudewa duba da yacce bukatar zama shugaban kasa take kara yawa a zukatan jagororin Najeriya musamman na Arewa.

Jagorori irinsu Major Hamza Al- Mustapha, Tambuwal, Sule Lamido, suna da matukar sha’awar darewa karagar mulkin Najeriya.

Sai dai masana harkokin siyasa suna yi musu kallo irin na taron tsintsiya ba shara.

Ko a shekarar 2019 da ake ganin babu wanda zai kai labari wajen karawa da shugaba Muhammadu Buhari, adadin wadanda suka nuna aniyarsu ta neman kejarar shugabancin kasar suna da yawa.

Alhaji Atiku Abubakar da Engr Kwankwaso, sune wadanda akayiwa kallon iya kokarta karawa da shugaba Muhammadu Buhari, duk da cewa anfi dora tasirantuwar Atiku Abubakar akan Engr Kwankwaso bisa dalilin goyon bayan mutanen kudancin Najeriya da Kwankwaso ya rasa.

Masana sun kara bayyana cewa; Atiku ya samu goyon bayan mutanen kudancin Najeriya bisa matsayin daya taka, Atiku ya zamewa mutanen Kudu dole bawai don soyayya ba, sai dan rashin kaunarsu da shugaba Muhammadu Buhari tare da suna ganinshi a mutumin da bashi da tsananin kishin yankin Arewa.

Zuwa yanzu, za’a iya cewa dambarwar ta kare tsakanin shugaba Buhari da Alhaji Atiku Abubakar bayan da shugaba Buhari ya lashe zabe a akwati da kuma kotun zabe kuma shugaba Buhari bazai sake takara ba.

Duba da yanayi da kwadayin mulki na Atiku Abubakar, kashi 90 bisa 100 ya nuna zai kara fitowa takara a zaben 2023, domin yana ganin bayan shugaba Buhari babu wanda zai iya takara da shi (Atiku) ya kai labari.

Ko mutanen Arewa zasu so Kwankwaso kamar Buhari?

Goyon bayan mutanen Arewa ne kawai zai saka Kwankwaso zamewa shugaban Najeriya bisa dalilin cewa;

Bangaren Yarabawa, bazasu taba ajiye Bola Ahmad Tinubu, wanda yake a matsayin jagoran siyasar yankin, domin su goyawa Kwankwaso baya ya zama shugaban kasa ba. Kuma ko ya dauki mataimaki a yankin, sai dai suyi masa “‘yar burum-burum.”

Bangaren Inyamurai, basa son Kwankwaso dalilin tambarin Kishin Arewa da suka buga a kirginshi, wanda haka yasa suke ganin bai chanchanci su goya masa baya ya gina yankinshi na Arewa kadai ba.

Sai dai daukar mataimaki a yankin zai kawo rarrabuwar kai a tsakaninsu, ta inda zai iya samun kaso dayawa a yankunan Inyamuran wanda idan ya hada da na Arewa baki daya, zasu bashi damar zama shugaban Najeriya.

Idan hakan ta faru, zamu iya cewa kalmar “Daga Daura sai Madobi” da take ta yawo a gari zata tabbata.

AMD

Masu Alaka

Ra’ayoyi: Jahilci ne amfani da kalmar ‘Hassada’ a siyasa

Dabo Online

Shugabanci ne matsalar Najeriya da Arewa, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Alakar dan Majalissar tarayya na Fagge da Al’ummar da yake wakilta, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso?

Dangalan Muhammad Aliyu

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

Dabo Online

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso a fafutukar darewa kujerar Lamba 1?

Dabo Online
UA-131299779-2