Home LabaraiGanduje ya sake nada Ali Baba Agama Lafiya a matsayin mai bashi shawarar addinai

Ganduje ya sake nada Ali Baba Agama Lafiya a matsayin mai bashi shawarar addinai

by Dabo Online
0 comments
Ali Baba Agama Lafiya

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabuwar shugaban ma’aikatan jihar Kano tare da masu baiwa bashi shawara na musamman guda 5.

Gwamnan ya bayyana hakane cikin wata sanarwa da mai magana da yawunshi, Abba Anwar, ya rabawa manema labarai.

Gwamna ya nada Hajiya Binta Lawan Ahmad, a matsayin shugabar ma’aikatan gwamnati na jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewa gwamnan ya sake nada Alhaji Ali Baba Agama Lafiya Fagge, a matsayin mai bashi shawara na musamman akan harkokin addinai, Alhaji Mustapha Buhari (Ba kwana) a matsayin mai bada shawara kan sha’anin siyasa.

Sauran sun hada da, Hamza Usman Darma, mai bada shawarar ayyuka na musamman, Tijjani Mailafiya Sanka, (Majalissar Sarakunan Kano) da kuma Yusuf Ali Tumfafi.

Sanarwar tace zasu fara ayyukansu a nan take.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00