Yanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a yau alhamis gamayyar kungiyoyi fiye da 35 sunyi kira da ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ba tare da bata lokaci ba.

Rahoton mu na Dabo FM ya rawaito mai magana da yawun gwamnan, Malam Abba Anwar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa da PremiumTimes.

Anwar yace “Gamayyar kungiyoyin sunyi kiran ne bayan da suka bayyana Sanusi da cewa yana kokarin ya kafa wata jihar a cikin jihar Kano.”

Kamar yadda shugaban gamayyar kungiyoyin ya rattaba hannu kan takardar da suka aikewa gwamna Ganduje.

Masu Alaƙa  Tsugunno: Masu nadin Sarki a masarautar Kano sun maka Ganduje a kotu

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.