Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Ganduje ya siyo motoci kalar ‘Kwankwasiyya’ guda 100 na zirga-zirga a jihar Kano

1 min read

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi ya kawo motocin sufuri guda 100 domin zirga-zirga a jihar Kano.

Kamar yadda Gwamnan ya bayyana a watanni bayan, na kawo motocin domin saukaka zirga-zirga a jihar bayan dawowarshi daga kasar Saudiyya.

Farkon jerin motoci 100 zasu fara aiki a tashoshi 2 na jihar wanda ya hada daga Titin Gwarzo zuwa Bata da kuma Daga Dawanau zuwa Bata.

Mataimakin gwamnan a fanni labarai, Salihu Tanko Yakasai motocin zasu fara aiki ne a watan Augustan shekarar 2019.

Motocin dai hadin gwiwa ce tsakanin gwamnatin jihar Kano wacce take da kaso 35 inda kuma su ‘yan kasuwar da suka zuba jarin suke da kaso 75.

Gwamnatin ta bayyana zata fara gwajin motocin nan bada jimawa ba, kuma ta bada tabbacin gina tashoshin motocin a cikin wata 3.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.