Copyrighted.com Registered & Protected

Gobe Alhamis, Buhari zai tafi kasar Saudi Arabia

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa kasar Saudiyya a gobe Alhamis kamar yadda sanarwa ta gabata daga fadar gwamnatin.

Gwamnatin tace shugaban zai amsa gayyatane wacce Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz, ya aike masa da ita tun watanni da suka wuce.

Buharin zai shafe kwanaki 7 domin gudanar da Umara kamar yadda mai magana da yawunshi Mal Garba Shehu ya bayyana.

%d bloggers like this: