Copyrighted.com Registered & Protected

Nine Malamin Sanata Kwankwaso a Siyasa – Musa Iliyasu Kwankwaso

Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Hon Musa Iliyasu Kwankwaso yace shine ya fara shigar da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso siyasa lokacin da yana matsayin mataimakin Darakta a Ma’aikatar Ruwa ta jihar Kano

Musa Iliyasu yayi ikirari cewa shine ‘Mai Gidan’ Kwankwaso a siyasance. Yace shine ya tabbatar da Kwankwaso ya zama dan siyasa duk da irin kalubalen da suka fuskanta a lokacin.

Da yake bayyanawa a hirarshi da Jaridar New Telegraph, Musa Iliyasu yace shine wanda yayi ruwa yayi tsaiko tare da nacewa kan lallai Kwankwaso ya shiga cikin shiyasa.

Musa Iliyasu ya kara da cewa shine wanda yasa Kwakwason ya zamo dan siyasa mai kishia tin a wancan lokacin da yana aiki a hukumar Ruwan jihar Kano.

Yace, “Nine shugaban Matasa a wancan lokacin, muna cikin siyasar tsundum, ya kawo Rabi’u Musa Kwankwaso, har abin ya zama cece-kuce akan waye shi.”

Masu Alaƙa  Biyan Albashi: Bance kar a biya ma'aikata N30,000 ba - Kwankwaso

Ya bayyana cewa bisa dalilin tasirin siyasar (Musa Iliyasu) da yake da ita a wancan lokacin, ya tsayar da Rabi’u Kwankwaso takarar kujerar majalissar tarayya kuma har ya kai ga samun nasara.

Iliyasu, ya tabbatar da cewa irin siysar da Sanata Kwankwaso yake yi a yau, ba irinta aka koya masa ba.

Daga karshe Musa Iliyasu yace Rabi’u Kwankwaso bai taba cin zabe na gaskiya ba, ya bayyana cewa dukkanin zabubbukan da Rabiu Kwankwaso ya lashe sai da ya tafka magudi.

“Har wannan zaben da aka gudanar na karshe, yayi hayar baki daga Kaduna dama sauran wurare suka shigo Madobi don suyi magudi, amma da ikon Allah, mutane suka tashi tsaye wajen a kare faruwar hakan.”

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: