Rahotannin sun bayyana cewa tini dai gwamnatin tarayya ta karbi umarnin daga kotu a Abuja na bayyana kungiyar IMN da Al-Zakzaky yake jagoranta a matsayin kungiyar ta’addanci.
Tin dai a ranar 26 ga watan Yulin 2019, mai shari’a Nkeonye ta ayyana haramta kungiyar tare bayyanata a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kotun ta kuma bawa gwamnati umarnin fitar da sanarwar haramcin kungiyar tare da wallafawa a manyan jaridun kasar guda 2.
Dokar ta hana dukannin wani mutum ya bayyana kanshi a matsayin dan kungiyar tare da haramta dukkanin amfani da sunan kungiyar a kowanne irin lamari.
Gidan Talabijin na Channels a rawaito cewa; ta samu tabbaci daga ofishin ministan shari’a na kasa cewar “Tini dai sakataren ofishin, Dayo Akoata ya fitar da takardar haramcin kungiyar ta Shi’a kamar yacce kotu ta bukata.
