Zaben Kano: “Abba Gida-Gida” ya shigar da kara bisa rashin amincewa da zaben Gwamna

Karatun minti 1

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Engr Abba K Yusuf “Abba Gida Gida” ya shigar da kara kotu zabe a yau Alhamis.

Abba, ya kalubalancin zabe da yacce aka gudanar dashi. Zaben da ya kira fashi da makami irin na shiyasa.

Ranar 23 ga watan Maris dai hukumar zabe ta kammala gudanar da karashen zaben 9 ga wata bisa kiran zaben 9 ga watan wanda bai kammala ba.

PDP tace taki amincewa da zaben ne saboda anfani da bata gari wajen hana mutane suje su kada kuri’arsu, tare da cewa zaben yana cike da kura kurai ciki harda rigima da hargitsi wanda yayi sanadiyyar mutane da dan dama. – A cewar PDP.

Sai dai a nata bangaren, rundunar ‘yan sandar jihar Kano, karkashin jagorancin DIG Anthony, ta bayyana zaben a matsayin wanda akayi lafiya aka gama lafiya.

A zaben farkon “Abba Gida Gida” ne ke jan gaba da ratar kuri’a 26,000, inda bayan ranar 23 ga wata, ranar da aka kammala zabe, Gwamna Ganduje ya biya bashin ratar Abba tare da wuce shi da kuri’u kimanin 9000.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog