Copyrighted.com Registered & Protected

Gobara a Kannywood: Mun sasanta da Mustapha Nabruska – Hadiza Gabon

Fitacciyar Jaruma a masana’antar fim ta Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, tace sun sasanta da jarumi Musatapha Nabruska.

Hakan na zuwa ne bayan da jarumar ta karyata labarin da sashin Hausa na Jaridar Leadership ya wallafa na cewa jaridar ta cafke jarumar bayan umarnin da kotu ta fitar na kama jarumar a makonnin da suka gabata.

Jarumar tace ana watsa labaran ne domin bata mata mutuncinta a idon duniya.

Da take magana da manema labarai a jihar Kano, Hadiza Gabon ta bayyana cewa karya ake yi, kuma babu wata hukuma data kama ta.

“Jami’an ‘yan sanda basu kama ni ba, rahotanni da labaran da ake yadawa duk anayi ne a yunkurin da ake na bata min suna.”

Masu Alaƙa  Kotun ta bawa CP Wakili umarnin kama Hadiza Gabon

“Yanzu a maganar da nake daku, mun sasanta da Nabraska, wanda ya kai ni kotu, don haka ina mamaki a ina aka samu labarin an kama ni. Kotu ta rika ta janye umarnnin data bayar.”

Gabon ta kuma kara karyata labarin da ake cewa, ta tsugunna har kasa ta nemi ya yafe mata kuma ya taimaka mata ya janye karar daga kotun shari’a.

“Labarin karya ne kawai,ban tsugunna a gaban shi ba (Nabraska); mun zauna mun sasanta kanmu da kanmu.”

Masu alaka

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: