INEC ta tabbatar da Matawalle a matsayin zababben gwamnan Zamfara

Babbarhukumar zzabe ta INEC ta tabbatar da Matawalle a matsayin zabbaben gwamnan jihar Zamfara.

Shugaban INEC, Farfesa Yakubu ne ya sanar da haka a ranar Asabar 25/05/2019, a babban shedikwatar hukumar dake babban birnin tarayyar Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan da Kotu koli ta kwace nasarar da jami’iyyar APC tayi bisa rashin gudanar da zaben fidda gwani a jami’iyyar.

Farfesa Yakubu ya tabbatar da Ranar Litinin 27/05/2019 a matsayin ranar da zata baiwa dukkanin wadanda suka samu nasara bayan umarnin kotu a ranar Juma’a.

Babbar Kotun dai ta ce dukkanin kuri’un da jami’iyyar APC ta samu a zaben da aka kammala ya tashi a iska inda ta tabbatar da wadanda suke biyewa APC baya a matsayin wadanda suka lashe zabubbukan.

PDP ce ke rike da dukkanin Sanatoci 3 da ‘yan majalissun wakilai 7 da ‘yan majalissar jiha 24 na jihar Zamfara.

%d bloggers like this: